Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mai Unguwar Kawaje, dake Karamar hukumar Nasarawa a jihar kano, Alhaji Umar Ado, ya kasance cikin farin ciki da murna, yayin da ya cika Shekaru 50 a kan karagar mulki, inda ya tuna da rashin jin dadi da ya kasance a lokacin da yake mulkar akalla gidaje 500.
Da yake jawabi a yayin bikin, shugaban kwamitin gudanarwa wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, Dokta Bature AbdulAziz, tare da Sakatarensa, Alhaji Dahiru Musa, ya ce cikin shekaru 50 da suka gabata a karkashin jagoranci da sa ido mai Unguwar ta kawaji an sami cigaba ta fannoni daban-daban a yankin .
Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano ta Magantu Kan Bacewar Murjar Kunya a Gidan Yari
Bature AbdulAziz, ya ce a shekaru 50 da suka gabata babu wani Kamfani ko wata babban Kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a yankin, amma a yau akwai kamfanoni sama da 50 da ke aiki a kawaji, yayin da akwai sama da Makarantu sama da 50 kuma suna gudanar da ayyukan bada ilimi a duk a yankin.
Sakataren kwamitin, Dahiru Musa, ya yi nuni da cewa saboda hadin kai da kaunar juna da aka samu a yankin ya sa mutane da yawa suka bada gudunmuwa har aka sami nasarar yin wannan taro na cikar mai unguwar kawaji shekaru 50 akan karagar Mulki.