Yan Sanda Sun Kama Fasto Kan Safarar Yaran Arewa Zuwa Kudancin Najeriya

Date:

 

Rundunar yan sanda a Abuja sun kama wani fasto da wasu mutane biyu bisa zargin safarar kananan yara daga jihar Nasarawa zuwa Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a bayan da da farko ’yan sandan sun kama wani direban wata motar haya dauke da yaran 12, maza hudu da mata takwas.

Adam A Zango ya Bayyana Dalilan da Suka sa ya Daina Fitowa a Fina-Finan Kannywood

Kwamishinan ’yan sandan ya ce an kwaso yaran masu shekaru 5 zuwa 16 ne daga Akwanga a Jihar Nasarawa zuwa wani wuri da aka gano daga baya cewa Jihar Ogun ne.

 

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa dukkan yaran sun fito ne daga Karamar Hukumar Akwanga, kuma wani Fasto Simon Kado da Jesse Simon Kado da yanzu haka suna hannun ’yan sanda ne ke safarar su.

Shugabannin Kananan hukumomi 3 a Kano sun fice daga APC zuwa NNPP

Kuma yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, rundunar tana kokarin ganin ta mika wa rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa yaran domin hada su da iyalansu,” in ji shi.

CP Benneth Igweh ya jaddada aniyar rundunar wajen tabbatar da tsaron al’umma, sannan ya yi kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ba su aminta da shi ba ga lambobin kar-ta-kwana na rundunar: 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; 09022222352.

 

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...