Daga Aisha Aliyu Umar
Masu ababen hawa da ke bin manyan tituna a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan yadda jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA ke yawan rokon su kuɗi .
Jami’an KAROTA na yin shingaye a kan tituna a jihar yayin da wasu kuma suke tsayawa a hanyoyin gwamnatin tarayya da suka hada Kano da sauran jihohin.
Jami’an KAROTA yawanci suna tare hanya da tsofaffin tayoyi tare da jami’ansu wajen cin zarafi da karbar Kudade a wajen masu motoci.
Bayan Zanga-Zangar Lumana, Masu Sana’ar Gurasa a Kano Sun Bayyana Dalilan su na Tafiya Yajin Aiki
Hanyoyin da suka yi kaurin suna wajen ganin ayyukan KARATO sun hada da Maiduguri, Hadejia, Gwarzo, Zaria da Katsina Road, wadanda suka hada Kano da sauran jihohin da ke makwabtaka da su.
Wasu daga cikin masu ababen hawa da suka zanta da manema labarai bisa sharadin sakaye sunansu, sun ce a kullum sai sun tanadi kudin da zasu baiwa yan KAROTA domin gujewa cin zarafi daga gare su.
“Muna bayar da makudan kudade ga jami’an KAROTA wadanda suke tare manyan shingaye kan manyan tituna suna karbar kudi daga wajenmu ba tare da sanin wasu dalilai ba.
Jaruma Amal Umar ta Bayyana Alakarta Da Mawaki Umar M Shariff
A lokacin da tawagar ‘yan jarida ta ziyarci ofishin Manajan Daraktan KAROTA Faisal Muhmud domin tabbatar da zargin da ake yi musu, ya ki ya gana da yan jaridun, amma wani ma’aikacin ofishin da ya so a sakaya sunansa ya ce MD ba ya jin dadin yan jaridu suke zuwa Ofishin nasa domin tattaunawa da shi.
Daily Post