Al’ummar Yar Gaya, Jido, Dadin Kowa da Marmaraje sun roki gwamnan Kano ya kai musu dauki

Date:

Daga Zaharadeen Saleh.

Alummar garuruwan Yar Gaya da Dadin Kowa da Jido da Kuma Dadin Kowa dake yanking karamar hukumar Dawakin Kudu sun sun roki gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf da ya kawo musu dauki saboda yinkurin kwace musu gonaki da wasu mutane ke kokarin Yi.

Alummar sunyi wannan roko ne a lokacin da suka gudanar da wata zanga zangar lumana saboda rashin amincewa su a kokarin kwace musu gonaki da ake Yi.

Daya daga cikin mutane da suka Yi bayanin Malam Bashir Yar Gaya ya bayyana cewa suna rokon mai girma gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf daya kawo musu dauki gaggawa saboda wannan funkarfi da ake yinkurin Yi musu.

Malam Shekarau ya yi tsokaci Kan Kiran da Ganduje ya yiwa Gwamnan Kano na Komawa APC

Bashir Yar gaya yace sun wayi gari sun ga wasu mutane suna auna musu gonaki, Kuma sun tambaye su amma suka ce Jira nana gaba za’a Yi musu bayanin.

Wata mata mai suna Talle Ali tace tana kira ga gwamnan ya taimaki musu mijin ta ya mutu ya barta da ya’ya ashirin, da wadanan gonaki suka dogara dasu suke ci suke Sha Amma ana so a kwace musu.

Da dumi-dumi : Kotu Ta Bayyana Dalilin Mayar da Danbilki Kwamanda Gidan Yari

Shi ma ana sa bayanin mai unguwar Yar Gaya Haruna Hassan da yayi bayanin amadadin masu unguwanin garuruwan yace basu San komai ba haka wannan al’amari.

Haruna Hassan yace akwai bukatar gwamnan Kano ya kawo musu dauki domin ku butar da alummar wannan garuruwan daga halin furgice da suka Samu kan su a cikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...