Kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA ta sanar da matakin janye ayyukanta a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke jihar Kano har sai yadda hali ya yi, bayan da wasu ‘fusatattun mutane dauke da makamai’ suka far wa wani likita da ke bakin aiki.
Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakatarenta ya fitar.
ECOWAS ta Mayar da Martani Kan Ficewar Mali, Burkina Faso, Nijar daga Kungiyar
Sanarwar ta ce yan’uwan wata mata da ta ke jinya a asibitin ne suka tayar da hatsaniya inda suka boye likitan, sai dai daga bisani mahaifin likitan, wanda shi ma yake aiki a asibitin ya samu kubutar da ɗansa.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu, ba ta akai ga tantance abin da ya sa mutanen suka far wa likitan ba.
Kungiyar ta ce shugabanninta sun je wajen da lamarin ya faru inda suka lura da cewa akwai rashin isasshen tsaro a asibitin abin da ta ce babban kalubale ne ga ma’aikatan lafiya da ke aiki a asibitin.
Sakataren kungiyar ta NMA ya ce dalilin haka ne ya zama dole kungiyar ta janye mambobinta daga aiki cikin yanayi na rashin tabbas har sai hukumomin asibitin sun tabbatar masu da tsaro.
A cewar kungiyar, za su ci gaba da bibiyar yanayin tare da shawartar mambobinsu.
Yanzu haka dai Mutane na fuskanta matsalolin daban-daban sakamakon dakatar da aiyukan likitocin asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.
BBC Hausa