Uku daga cikin ƙasashen da sojoji suke jagoranta a yammacin Afrika sun ce za su fice daga ƙungiyar raya tattalin azriƙin yankin ta ECOWAS saboda takunkumin da kungiyar ta sanya musu.
Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da haka ne ta cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, suna cewa ECOWAS ta gaza taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.
Jarumar Hadiza Gabon Ta Yi Martani ga Masu Magana Kan Ramarta
“Bayan shekaru 49, gwarazan al’umar ƙasashen BUrkina Faso da Mali da Nijar sun yi takaicin yadda ECOWAS ta sauka daga kan turbar da aka kafa ta, kamar yadda Kanar Amadou Abdramane, shugaban da ke jagorantar sojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya karanta.
ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumai tare da dakatar da su daga daga ƙungiyar, biyo bayan kwace iko da sojoji suka yi a jerin juyin mulkin da suka yi, abin da ya haifar da fargaba ta ɓangaren siyasa a Sahel.