Daga Umar Sani Kofar Na’isa
Da safiyar yau Lahadi, Fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alh Muhammadu Iliyasu Bashar OFR, ta cika maƙil da mutane domin shaidar Auren Mutane 300 da Gwannatin Jahar Kebbi ta shirya ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar NANAS mallakin Matar Gwamnan Kebbi Haj Nafisa Nasir Idris.
Mutane ne daga kowane ɓangare na Jahar Kebbi aka ba damar wannan aikin alheri a Ƙananan Hukumomi 21 dake Jahar.
Gudunmawar da Bashir Gentile Ya Baiwa Pyramid Radio Zata Inganta Aiyukan mu – Gm Abba Bashir
Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine ya jagoranci wannan auren na Mutum 300 da suka haɗa da Marayu, Marasa Ƙarfi da Gwauraye.
Bayan an tantance kowane Ango da Amarya ta hanyar duba lafiyar su tun a kwanan baya, Shehin Malamin bisa ga umurnin Mai martaba Sarkin Gwandu ya bada damar a biya “Sadaki” kan Naira Dubu Saba’in (₦70,000) ga kowace Amarya, nan take aka bada damar ƙulla aure kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
Jarumar Hadiza Gabon Ta Yi Martani ga Masu Magana Kan Ramarta
Kowace Amarya zata samu Gado, Kujeru, Buhun shinkafa 25kg, Man gyaɗa, Kuloli Murhu da dai sauran kayayyakin aikin gida.
Haka zalika kowane Ango yasamu Shadda yadi 10 da kuɗin ɗunki.
Mai girma Matar Gwamnan Kebbi Haj Nafisa Nasir Idris Ƙauran Gwandu da Matar Mataimakin Gwamnan Kebbi Haj Maryam Umar Abubakar Tafidan Kabi da tawagar su duka sun halarci wannan bukin auren.
Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Kebbi, Rt Hon Usman Mohammed Ankwai ne ya waƙilci Mai girma Gwamna Dr Nasir Idris (Ƙauran Gwandu).
Alh Faruku Aliyu Yaro Enabo (Jagaban Gwandu) na daga cikin manyan jami’an Gwannati da suka halarci wannan auren. Kuma akwai Kwamishinoni da Mambobin Majalisar Dokoki na Jahar Kebbi, Sarakuna da Malammai da sauran jama’a.
An gabatar da nasihohi ga Ma’auratan na zamantakewa daga Malumma daban daban, haka kuma an ɗaura Auren cikin aminci da walwala.