Nasarar Da Super Eagles Ta Samu a AFCON Tamu ce , Zamu Cigaba da Tallafa Musu – Sen. Kawu Sumaila

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin wasanni Sanata Suleiman Kawu Sumaila OFR, ya yabawa Super Eagles bisa bajintar da suka yi aka wasan da suka yi da kasar Kamaru a wasan zagaye na 16 a gasar AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast.

Eagles ta lallasa babbar abokiyar hamayyarsu ta Cameron da ci 2-0 wanda hakan ya baiwa Super Eagles damar zuwa wasa na biyu da na karshe (Quarter Final) .

Shugaban ya ce kwazon da kungiyar ta yi a kan ‘yan Kamaru ya samu yabo daga dukkanin ‘yan Najeriya a duniya baki daya.

Gudunmawar da Bashir Gentile Ya Baiwa Pyramid Radio Zata Inganta Aiyukan mu – Gm Abba Bashir

“Mun ji dadi sosai ga yadda yan wasanmu suka nuna fasaha da kwazo yayin wasan “.

“Babu shakka sun baje kolin kwazo da fasaha, wanda hakan ya sa al’ummar kasar baki daya suka yi alfahari da abun da sukai.”

Kawu Sumaila yace nasarar da kungiyar kwallon kafan ta mu a gasar cin kofin Kasashen Africa ta farantawa miliyoyin ‘yan Najeriya rai, har ma ya karawa matasa masu sha’awar wasanni kwarin gwiwa.

Muna daukar matakan dakatar da dauke wasu hukumomin gwamnatin tarayya zuwa Lagos – Sanatocin Arewa

Daga nan ya bukaci kungiyar da su ci gaba da nuna kwazo wajen tunkarar sauran wasannin da suka rage a gasar har su sami nasarar dauko kofin .

“Muna da cikakken kwarin gwiwa kan kwarewar kungiyar kuma mun yi musu alkawarin ci gaba da samun goyon baya daga kwamitin majalisar dattawa kan harkokin wasanni da kuma daukacin majalisar dattawa ta 10”, in ji shi.

Ya kuma tabbatar wa kungiyar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya cewa ba za su rasa ko wane irin tallafi daga kwamitin wasanni na majalisar dattawa da ma daukacin majalisar dattawa karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa Sanata Godwill Akpabio ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam...