Daga Aisha Aliyu Umar
Hukumar gudanarwar gidan Radio tarayya Pyramid fm dake kano ta yabawa shahararren dan Siyasar nan kuma mai fashin bakin kan harkokin siyasar Alhaji Bashir Hayatu Gentile bisa futulu masu amfani da hasken rana guda 5 da bayar aka Sanya domin haskaka harabar gidan Radio.
” Baba shakka wannan abu da Bashir Gentile ya yi mana zai taimakawa ma’aikatan mu su gudanar da aikin su cikin nutsuwa, sannan zai inganta tsaron gidan Radio da kuma kawata gidan radio”.
Hakikanin Yadda Siyasar Kano Zata Kasance a 2027 – Daga Bashir Hayatu Gentile
Shugaban gidan Radio Pyramid Malam Abba Bashir ne ya yi yabon jim kadan bayan kammala aikin sanya futulun masu amfani da hasken rana, wadanda aka sanya su a harabar gidan Radio, jiya Asabar.
Yadda Gwamnan Kano ya baiwa wata mata hakuri bayan bugar Motar ta da ayarinsa sukai
” Babu shakka Mun amfana da zaman da muke da Bashir Gentile a matsayin abokin gidan Radio Pyramid, don haka muna yaba masa matuka, duk da dama ba yanzu ya fara ba, don ko a Shekarar da ta wuce sai da yayi kokarin yin mana rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, amma abun bai yiwuwa saboda yanayi inga muke akwai duwatsu masu girma”. Inji Abba Bashir
Shugaban gidan Radio Pyramid ya kuma yi kira ga yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati da masu hannu da shuni da su yi koyi da abun alkhairin da Bashir Gentile wajen tallafawa ma’aikatun gwamnati don inganta aiyukan su.
” Wannan gidan na Pyramid Radio na gwamnatin tarayya ne, amma kuma na yan jihar kano ne , saboda kowacce jiha a Nigeria anyi mata nata, don haka akwai bukatar al’umma su rika zuwa suna bamu gudunnawa saboda bafi yawan ma’aikatan gidan Radio yan asalin jihar kano ne”. A cewar shugaban gidan Radio
Malam Abba Bashir ya ce zasu cigaba da kyautata dangantaka tsakanin gidan Radio Pyramid da kuma sauran al’ummar jihar kano don Cika sharuddan da suka sanya aka samar da gidan Radio, na daga darajar al’umma da hada kan kasa.