Gwamnan Kano Abba Kabir Zai Yi Dokar Aiwatar da Aikin Gwamnati Ta Fasahar Sadarwa

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnatin jihar Kano na shirin samar da dokar da zata bada cikakkiyar damar aiwatar da tsarin gudanar da aikin gwamnati ta amfani da fasahar sadarwa a duk fadin jihar, domin saukaka ayyukan gwamnati da bunkasa fannin tattalin arzikin ta amfani da fasahar sadarwa.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a wajen rufe taron Majalisar Sadarwa, kirkira da fasahar sadarwa Karo na 11, wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya aikowa kadaura24, ya ce tsare-tsaren an samar da su ne da nufin tabbatar da daidaito, inganci, da kuma tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da harkokin kudaden gwamnati ta hanyar amfani da manhajoji don tabbatar da taka tsantsan wajen amfani da kudaden.

Hakikanin Yadda Siyasar Kano Zata Kasance a 2027 – Daga Bashir Hayatu Gentile

Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulki, gwamnan kano ya samu damar sake bude Cibiyar fasahar sadarwa da aka rufe, biyan albashi na hanyar zamani, inganta tsarin biyan kudin IGR da nufin toshe zurarewar Kudade da dai sauransu .

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci da a mikawa jihar Kano matattarar fasahar sadarwa ta NCC dake jihar domin yin amfani da shi yadda ya kamata, ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyukan da za su ciyar da jihar Kano gaba musamman ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki .

Ina Sane Na Ki Fito Da Sakamakon WAEC Dina —Buhari

Tun da farko, ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki ta fasahar sadarwa, Dokta Bosun Tijjani, ya ce an shirya taron ne bisa la’akari da ajandar sabunta fata ta Shugaba Tinubu, sanin karfin fasaha da kirkire-kirkire a matsayin masu samar da ci gaban tattalin arziki da kuma bunkasar tattalin arzikin Nigeria.

Ya ci gaba da cewa, domin a kara habaka sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar inganta samar da kayayyaki a sassa masu muhimmanci ta hanyar fasaha da kere-kere, an samar da wani tsari wanda ya kunshi ginshikai biyar na ilimi, manufofi, ababen more rayuwa, kirkire-kirkire, kasuwanci da jari.

Dokta Bosun Tijjani ya ce kowane ginshiki na da nasaba da manufofin gwamnati da kuma cudanya da sauran jama’a, wanda shi ne tushen dabarun ba da damar ci gaban tattalin arziki da ci gaban fasahar sadarwa a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...