Hakikanin Yadda Siyasar Kano Zata Kasance a 2027 – Daga Bashir Hayatu Gentile

Date:

Daga Bashir Hayatu Gentile, MNIPR, MIPRA, MIPSAs, ARPA.

Yayin da aka fara shirye-shiryen tunkara babban zaɓen shekara ta 2027, tuni an fara hasashen yadda yanayin siyasar zai kasance. Rahotannin na nuna cewa akwai kyakykyawan zaton za’a kulla tafiyar siyasa a tsakanin tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da shugaba Kasar Nigeria Tinubu.

Ana ganin Kwankwaso da yake jagorantar jam’iyyar NNPP idan suka hade da Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, saboda dimbin magoya bayan da yake da su a jihar kano, zai iya samarwa da Tinubu kuri’u wadanda suka zarce yawan kuri’un da jihohin Kudu maso Yamma suke samarwa a zaɓen shugaban kasa.

Ina Sane Na Ki Fito Da Sakamakon WAEC Dina —Buhari

Sai dai kuma yanayin siyasar Kano a shekarar 2027 ya nuna cewa zai banbanta idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata. Yanzu haka dai jihar na karkashin ikon wasu manyan ‘yan siyasa guda hudu, wadanda kowannensu zai iya cinye shiyya ko mazabarsa ga jam’iyyar siyasar da yake cikinta.

Tinubu Ya Magantu Kan Batun Dauke Fadar Shugaban Kasa Daga Abuja

Kano ta Arewa tana karkashin Sen Barau Jibrin, Kano ta tsakiya kuwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ke da rinjaye, Kano ta Kudu kuma Sanata Kawu Sumaila ne ke jagorantarta, sai kuma rukunonin masu rike da sarautun gargajiya, malamai, ma’aikatan gwamnati, da masu fada aji a Kano su kuma suna karkashin Sanata Mallam Ibrahim Shekaru.

Don haka duk wata hadaka ta kungiyoyi biyu da muka ambata a baya da suka samu goyon bayan Sanata Mallam Ibrahim Shekaru zai yi tasiri a wannan yanayi. Don haka ’yan siyasa ku yi hattara kada wasu ‘yan bangar siyasa su yaudare ku, Siyasar Kano a 2027 ba ta da tabbas.

 

 

Wannan rubutu ra’ayine na Bashir Hayatu Gentile, MNIPR, MIPRA, MIPSAs, ARPA .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...