Da dumi-dumi: Tinubu ya gana da Ganduje da shugabannin APC na Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

A ranar Alhamis din nan ne shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tawagar da ta kunshi shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kano a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Jagoran tawagar akwai Shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, wanda ya isa fadar Villa tare da tsohon mataimakinsa wanda ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga Maris, Dr. Nasir Yusuf Gawuna.

Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da kotun koli ta yanke hukuncin tabbatar da babban abokin hamayyar Gawuna, Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP, a matsayin zababben gwamnan jihar.

Ganduje Ya Caccaki ‘Yan Siyasa Kan Lamarin Zaɓe a Najeriya

A watan Maris din da ya gabata ne dai mulki aka gudanar da zaben gwamnan kano, Inda Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 890,705 yayin da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, hakan tasa INEC ta bayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Abba Gida-gida ya Fadi Rawar da Kwankwaso ya Taka a Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano

A ranar 12 ga watan Janairu ne kotun koli ta mayar da Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano, inda ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ba a bayyana ajandar taron na ranar Alhamis ba kuma wadanda suka halarci taron ba su yi magana da manema labaran fadar gwamnati ba har yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...