Daga Khadija Abdullahi Aliyu
An gurfanar da Ahmad Dahiru Maiwuddadu, wanda ya rike mukamin kakakin Abdussalam Abdulkarim A.A Zaura, dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben da ya gabata, a gaban babbar kotun majistare ta jihar Kano mai lamba 19.
Ana zarginsa da bata sunan Sanata Rufa’i Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta kasa da kuma tada hankalin jama’a.
Justice watch ta rawaito ana zargin Maiwuddadu da bata sunan Sanata Hanga a wani shiri na gidan rediyo mai taken ‘Tauraron A.A Zaura’ wanda A.A Zaura ya dauki nauyi.
Kyautar Motar da aka Baiwa Jarumar “Labarina” Yasa Marubutan Kannywood Kokawa
Mai gabatar da kara, Barista Fatima Adamu Ahmad, ta yi zargin cewa wanda ake karar ya kira Sanata Hanga a matsayin mashayin giya wanda ya wawure kudin mazabar karamar hukumar birni tare da kashe su a gidajen giya.
Mai gabatar da kara ta bayyana cewa wadannan laifukan da ake zargin maiwuddadu sun sabawa sashe na 393 da 144 na dokar manyan laifuka.
Sai dai Maiwuddadu ya musanta aikata laifukan.
A zaman kotun, lauyan da ke kare Wanda ake tuhuma Anthony Agugu ya bukaci kotun da ta bayar da belin Maiwuddadu, bisa la’akari da wasu sassan na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ambato da kuma dokar shari’a ta jihar Kano, 2019.
Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo
Lauyan mai gabatar da kara bai soki bukatar belin ba, inda yace bayar da belin ikon kotun ne kadai.
Alkalin kotun, Binta Galadanchi, ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi naira dubu dari biyu, tare da wasu amintattun mutane biyu wadanda za su kasance ma’aikatan gwamnati masu Matakin albashi na 12 da kuma hakimin ko Unguwa.
Daga nan mai Shari’a Binta Galadanci ta dage sauraren karar har zuwa ranar 29 ga Fabrairu, 2024, don ci gaba da Shari’ar.