Kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi da kwacen waya na Jihar Kano ya kafa kotun tafi-da-gidanka domin gaggauta hukunta masu laifi.
Shugaban kwamitin, Birgediya Gambo Mai’Adua (mai ritaya) gargadi masu yi cewa du daina ko su gamu da fushin hukuma, domin gwamnatin jihar ba za ta lamuci ayyukansu ba.
Yanzu-yanzu: Barawon da ya kwaci waya Mota ta buge shi a Kano ya mutu – Yan sanda
“Kwamitin yana da kotun tafi-da-gidanka kuma yana da niyyar gyara dabi’un wadanda suka daina da kuma mayar da su cikin al’umma,” in ji shi.
Gambo Mai’Adua ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan yakin da kwamitin ke yi na yaki da shan miyagun kwayoyi da satar waya a jihar.
A cewarsa, akwai abin damuwa a cikin wani rahoto na baya-bayan nan da ke nuna a duk mutum shida a jihar, daya na shan miyagun kwayoyi, don haka gwamnatin jihar ta kaddamar da yaki da duk masu hannu a cikin lamarin.
Sarkin Kano Ya Magantu Kan Nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Ƙoli
Ya bayyana cewa kwamitin yana aiki tare da sauran hukumomin da ke aiki kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran laifukan masu alaka da su, don ganin an shawo kan yawan shan miyagun kwayoyi a Jihar Kano.
“Yaki da wadannan matsalolin hakki ne na kowa da kowa. Magance wannan barazanar tun yanzu shi ne abu mafi alheri gare mu da al’ummarmu,” in ji shi.
Jami’in kuma yi nuni da cewa, kwamitin zai mayar da hankali wajen farfadowa, sauya tunanin, da kuma dawo da wadanda abin ya shafa cikin al’umma idan sun daina.