Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya amince da nadin shahararrin dan Wasan Hausa na masana’antar kannywood Ali Nuhu a matsayin shugaban hukumar Fina-Finai ta kasar.
Naɗin nasa na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a.
Cikakken Bayanin Hukuncin da Kotun Ƙoli ta Yanke Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Ali Nuhu dai ya yi fice a harkar fina-finai a Kannywood da Nollywood.
Bayan Ali Nuhu akwai wasu mutane goma (10) da shugaban kasar ya nada su a wasu hukumomi da ma’aikatu dake karkashin ma’aikatar al’adu ta Nigeria.
Sanarwar ta bukaci wadanda aka nada din da suyi amfani da kwarewarsu wajen ciyar da hukumomin da aka tura su gaba.