Cikakken Bayanin Hukuncin da Kotun Ƙoli ta Yanke Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano

Date:

 

A yau Juma’a 12 ga Janairu 2023 Kotun Koli ta tabbatar da Gwamnan Kano Abba Kabir Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a kan kujerarsa.

Kotun ta soke hukunce-hukuncen da kotunan baya suka yanke na kwace kujerar Abba da kuma ba wa babban abokin hamayyansa, Nasir Yusuf Gawuna jam’iyyar APC.

Kotun Koli ta sanar da hukuncin ne bayan yi watsi da kararrakin da APC ta shigar na zargin aringizon kuri’un bogi dubu 165 da kuma ikirarin cewa Abba ba halastaccen dan NNPP ba ne, da ke da hurumin shiga zaben na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC a Kano Ta Magantu Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli

Alkalin da ya karanta hukuncin, Mai Shari’a Inayng Okoro, ya sanar cewa kotun daukaka kara ta yi kuskure wajen soke kuri’un Abba da ake takaddama a kan sahihancinsu, hasali ma, babu hujjar da ta tabbatar cewa ba su ne aka jefa a zaben ba.

Hakazalika, alkalan na kotun kolin sun sanar cewa batun zaman Abba dan takarar gwamna a NNPP abu ne na cikin gidan jam’iyyar, don haka wanda ba dan jam’iyyar ba, ba shi da hurumin kalubantar zamansa dan takarar jam’iyyar.

Da yake soke hukunce hukuncen na farko, Mai Shari’a Okoro ya shawarci alkalai da su rika yin duba na tsanaki kan kararrakin da aka kawo gabansu kafin su yanke hukunci.

Yanzu-yanzu: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir a matsayin Gwamnan Kano

Hukuncin kotun karshen na zuwa ne kawanaki 298 da zaben Gwamnan Kano, wanda aka shafe sama da makonni 40 ana shari’a a kansa.

Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano tana kalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna a ma Abba.

Gwamna Abba da NNPP ne suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a wannan shar’a mai cike da rudani ne domin ƙalubalantar ƙwace kujerarsa da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta yi.

Suna kuma kalubalantar yi da kuma shirinta na sauya rubutaccen hukuncinta — mai karo da juna — da ya tabbatar masa da kujerar.

Karo na biyu ke nan da gwamnan Kanon ke daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya da suka kwace kujerarsa.

Shari’ar zaɓen dai ta shafe sama da kwanaki 300 tana ɗaukar hankalin jama’a, musamman ma bayan kundin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya kan shari’ar ya fito ɗauke da saɓanin hukuncin da aka karanta a zamanta.

 

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...