Daga Abubakar Lawan Bichi
Mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da shiyar Bichi AC Yusif Dahiru Alkali ne ya bayyana cewa ba za su saurarawa duk wanda ya karya doka bayan kotun kolin Nigeria ta yanke hukuncin Shari’ar Zaɓen gwamnan jihar kano..
AC Yusuf Dahiru ya bayyana hakan ne yayi taro da Kungiyoyi da masu ruwa da tsaki na Kananan hukumomin dake Karkashin Shiyar Ofishin Yan sanda na Bichi.
AC Alkali yayi kira da iyaye dasu jawa ya’yan’su konne wajan bin doka da oda yayi sanar da hukunci zabe Gwamna da Kuma bayan hukunci zabe.
Mataimakin kwamishinan yace ana fakewa da murna daga karshe takoma fadace-fadace , don haka yace baza su lamunci hakan ba a gobe juma’a. Ya kuma tabbatar wa jama,a cewa kofar yan sanda abude take ba dare ba rana domin karbar rahotanni da zasu taimakawa rundunar.
Tarihin Alƙalin Da Zai Jagoranci Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Yakuma Shawarci iyaye dasu kara sanya idanu akan ya’yansu ya kuma ja hankalin yan siyasa da su guji dukkanin abinda zai kawo tada zaune tsaye a tsakanin Jama’a.
Anasa jawabin Shugaban kwamitin kyautata Alaka yan sanda da jama,ar Gari Mallam Garba Tukur, ya ce ashirye suke dasu bayar da dukkanin gudummawa domin Samar da cikar Tsaro a Shiryar ta Bichi
Ya kuma yi kira da yan siyasa dasu rugumi kaddara akan abinda zasuji na hukuncin da kotu Kolin.
Shari’ar Kano: Kotun Ƙoli ta Tsayar da Ranar Yanke Hukunci
Karshe Ya bukaci Shuwa gabannin dasuka zo sukoma suwayar wa jama,arsu kai akan zaman lafiya a tsakanin jama’a
Yayi taro Shuwagabanin kungiyoyin sunnuna jin dadinsu akan yadda Mataimakin kwamishinan ya karbesu.