Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kotun Kolin Nigeria ta ce ta sanya ranar Juma’a 12 ga Janairu, 2024 a matsayin ranar da zata yanke hukuncin kan shari’ar zaben gwamnan jihar Zamfara.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da kotun kolin ta aikewa lauyoyin bangarorin biyu.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Jam’iyyar APC da dan takarar ta na gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ne suka daukaka kara zuwa kotun kolin don kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.
Malam Shekarau Ya Yiwa Abba da Gawuna Nasiha Kan Hukunci Kotun Ƙoli
Ita dai kotun daukaka karar ta bukaci a sake zabuka a wasu mazabu dake jihar, lamarin da jam’iyyar APC tace bata lamunta ba hakan tasa ta garzaya kotun kolin.
Hukuncin kotun kolin dai shi ne zai kawo karshen ja’in jar da ake yi tsakanin jam’iyyar APC da PDP dake mulkin jihar karkashin gwamna Lawan Dare.