Daga Shehu Husaini Getso
Wani fitaccen manomi a yankin karamar hukumar Gwarzo Alh Abubakar Usman Tabanni ya bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi da su duba mawuyacin halin da al’ummar Nigeria suke ciki na tsadar kayayyakin abinci domin saukaka musu.
Alh Usman Tabanni yace tun ba’aje da nisa ba, a yanzu haka buhun masara a jihar Kano yana dosar zunzurutun kudi har Naira dubu Hamsin, wanda hakan yasa magidanta da dama basa iya ciyar da iyalinsu.
Alh. Abubakar Usman ya bayyana hakan ne lokacin da yake zanyawa da wakilin jaridar kadaura24 a Gwarzo, Kano.
Yace akwai tashin hankali kwarai da gaske ta yadda farashin kayayyakin abinci ke hauhawa kusan a kowacce rana a Nigeria.
“Hanya daya kawai da gwamnati zata iya shawo kan wannan matsala, ita ce kokarin wadata manoma da takin zamani a farashi mai rangwame, ta yadda manoma zasu sami saukin makudan kudaden da suke kashewa a harkokinsu na aikin gona”. Inji Alhaji Abubakar
Malam Shekarau Ya Yiwa Abba da Gawuna Nasiha Kan Hukunci Kotun Ƙoli
A cewarsa yana ganin don a sami nasarorin da ake bukata wajen tallafawa manoma, babu wata hanya da tallafin gwamnatoci zai dinga zuwa wajen manoma, fiye da tsarin shigo da masu sarautar gargajiya a cikin tsarin dari bisa dari, tunda su suka san manoma na hakika aduk inda suke.
Alh Abubakar Usman Tabanni ya yabawa Shugabanni da wakilan Yankin Kano ta Arewa a gwamnatin tarayya, bisa kokarin raya yankunan karkara,daga nan sai yayi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi kokarin tabbatar da aikin titin daya tashi daga Getso ya shiga Zangon Mallam Gwani,dan-Nafada, yan-kwanci, katsalle da sauran garuruwan dake wannan rukuni domin saukakawa manoma ta fuskar harkokin sufuri.