Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gada mai hawa uku da zata lashe Naira biliyan 27 da ta kai darajar Naira biliyan 27 a mahadar Dan’agundi, da kuma Tal’udu duk a cikin birnin Kano.
A wajen aza harsashin ginin, gwamnan ya ce an fara gudanar da manyan ayyukan ne domin rage cunkoson ababen hawa, da saukaka zurga-zurga, da kawata birnin, da hana gurbatar muhalli, da samar da ababen more rayuwa ga al’umma .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin tofa ya aikowa kadaura24.

Yayin da yake aza harsashin ginin, Gwamnan ya nanata alkawuran gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar tare da kudurin samar da karin ribar dimokuradiyya musamman ga wadanda aka zalunta.
Ya ce Kano a matsayinta na babban birni ta cancanci a samar da gagarumin sauyi na ababen more rayuwa domin biyan bukatun mazauna birnin sama da miliyan goma da inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna birnin.
Kotu a Kano Ta Gargadi Khalid Ishaq Diso Game da Shugabancin Karamar Hukumar Gwale
Gwamnan ya kara da cewa, kasafin kudin shekarar 2024 da ya riga ya sanya wa hannu ya zama doka an ba shi fifiko kan manyan ayyuka da zai dauki kaso 60% cikin 100.
Alh Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga dan kwangilar da ke gudanar da aikin da ya tabbatar da kammala aikin a kan lokaci, bin ka’idojin kwangila, amfani da kayan aiki masu inganci domin gwamnati ba za ta lamunci ha’inci ba.
Gwamnan yayi Karin haske game da batun kudaden da za’a gudanar da aikin, inda ya ce ya kasance al’ada ce daga magabata wajen gudanar da irin wadannan manyan ayyuka ta hanyar asusun hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke gudanarwa.
Ya kuma yi kira ga mutanen da ke amfani da hanyoyin aikin da kuma na kusa da wuraren da za’a gudanar da aikin, da su yi hakuri kan rashin jin dadin da ayyukan zasu haifarwa tare da tabbatar da cewa ana shirin samar da wasu hanyoyin da za a bi domin saukakawa al’umma wajen zirga-zirga.