Za a fara biyan matasa kimanin Naira Dubu arba’in idan suka amince a yi musu rigakafin korona

Date:

Wata jiha a Amurka ta ce za ta bai wa matasa tukwicin dalar Amurka 100 kwatankwacin kimanin naira dubu arba’in idan suka amince aka yi musu allurar rigakafin korona.

Jihar West Virginia ta ce tana fatan ba da tukwicin ga yan shekara 16 zuwa 35 domin basu kwarin gwiwar zuwa a yi musu allurar.

A cewar gwamnan jihar, Jim Justice, matasa suna da rawar takawa a yaƙi da annobar ta korona.

Jihar tana daga cikin jihohin Amurka da aka tsara yi wa jama’a da yawa allurar rigakafin sai dai lamarin ya fuskanci tsaiko a baya-bayan nan.

Akwai fargabar cewa matasa na iya nuna rashin damuwa da zuwa yin rigakafin.

Ba da kudin na nufin mutanen da aka yi wa allurar da ke cikin rukunin za su iya samun dalar Amurka 100 da riba a wani lokaci nan gaba.

Za kuma a bai wa duk wanda shekarunsa suka kai 16 zuwa 35 da tuni aka yi musu allurar.

West Virginia ce jihar da ta fi yawan masu cutar korona a Amurka a cewar Jaridar New York Times.

BBC Hausa ta rawaito Kashi 52 cikin 100 na mutum miliyan daya da rabi sun yi allurar sau ɗaya a cewar Gwamna Justice amma ya kara da cewa wasu kashi 40 na al’ummar jihar na iya yin baya-baya wajen zuwa a yi musu rigakafin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...