Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da daga likkafar Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo daga mukamin babban jami’in tsare-tsaren gwamna zuwa Darakta janar.
A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mai magana da yawun gwamnan ya ce nadin na Hon. Rogo ya fara aiki ne nan take .

Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo wanda tsohon shugaban karamar hukumar Rogo ne kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar Kano an fara nada shi a matsayin shugaban tsare-tsare a lokacin mika mulki na Gwamna sannan ya ci gaba da rike mukaminsa bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba da gaske take ba wajen yiwa musulmi adalci – Falakin Shinkafi
Hakazalika Gwamnan ya amince da nadin Hajiya Nana Asmau Jibrin a matsayin Darakta Janar ta Bincike da Adana bayanai a Gidan Gwamnatin Kano.
Nana ta kasance mataimakiyar daraktan yada labarai ta kungiyar yakin neman zaben Gwamna Abba tun daga shekarar 2022.
Ta kammala digirinta na farko da na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa, Asmau ƙwararriyaryar jarida ce wacce ta shafe shekaru 20 tana aiki a kafofin yada labarai.
Sanarwar tace gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya su murna, sannan ya bukace su da su jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.