Sanatocin Najeriya sun sadaukar da albashinsu ga mutanen da harin harin bom ya shafa

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Sanatocin Najeriya gaba dayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri.

Talla

Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama Naira miliyan 109.

Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru.

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba da gaske take ba wajen yiwa musulmi adalci – Falakin Shinkafi

Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya mika godidyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya bukaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci.

Ya kumu nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko kabilanci a kan abin da ya faru, inda ya ce abin ba haka yake ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...