Mutanen Shinkafi sun yi bata kashi da yan Bindiga

Date:

Yan bindiga a yau sun sake kai hari Karamar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara, inda suka yi artabu da mutanen garin, kafin daga bisani a tura jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar dake karkashin wani da ake kira Kachalla Turji sun kai harin ne domin tirsasawa mutanen Shinkafi kin amincewa da sabbin dokokin da Gwamna Bello Matawalle ya saka domin dakile hare haren da ake samu a fadin jihar.

Daya daga cikin shugabannin garin Suleiman Shuaibu Shinkafi ya shaidawa RFI Hausa cewar anyi artabu sosai tsakanin mazauna Shinkafi da ‘Yan bindigar kafin zuwan tawagar sojoji da ‘Yan sanda abinda ya sa barayin suka gaggauta janyewa daga garin.

Shinkafi yace mazauna garin sun yi nasarar kashe daya daga cikin ‘Yan bindigar kafin janyewar su, yayin da suma suka harbi mazaunin garin guda.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar hare haren ’Yan bindiga dake sace shannu da mutane, tare da hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.

Ko a talatar nan ‘Yan bindigar sun sace dalibai maaz ad mata sama da 70 a Kayan Maradun lokacin da suke zana jarabawa, kasa da mako guda bayan sakin daliban kwalejin aikin gona dake Bakura.

Wannan ya sa Gwamna Matawalle rufe daukacin makarantun jihar da hana cin kasuwannin mako-mako da saka dokar hana fitar dare da kuma hana sayar da man fetur da yawa ga jama’a, matakin da ya girgiza ‘Yan bindigar.

170 COMMENTS

  1. It’s one of the easiest posts I had to make… and I have not asked for comments but boom! it’s one of my most popular posts in terms of comments.
    But small web sites with limited readership shouldn’t get too upset if they aren’t overflowing with comments. Not every reader is going to have something to say about every post and the fewer readers, the less chance of a comment.
    카지노사이트

  2. Обязательный претендент на титул WBO в супертяжелом весе Александр Усик внимательно следил за чемпионом мира по версиям WBA, WBO и IBF Энтони Джошуа на Олимпиаде 2012 года в Лондоне, сообщает Sky Sports. Энтони Джошуа Александр Усик Джошуа: Усик вміє боксувати, він серйозний претендент – Бокс

  3. Український важковаговик Олександр Усик (18-0-0, 13 ko) зустрінеться в чемпіонському поєдинку за титули wbo, ibo, ibf із британцем Ентоні Джошуа (24-1-0, 22 КО).Поєдинок заплановано на 25 вересня на стадіоні Тоттенгем Готспур Арена в Александр Усик Энтони Джошуа 2021.25.09 Усик вирушив до Лондона на бій із Джошуа – Новости Спорта

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...