Shugaba Tinubu ya Magantu Kan Matsin Rayuwar da ‘yan Nigeria Suke Ciki

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwmnatinsa na gudanar da tsare-tsare da manufofi da nufin samar wa ‘yan ƙasar ci gaba mai ɗorewa

Shugaban ƙasar ya ce ƙasar na buƙatar sadaukarwa domin samun ci gaba.

Yadda Wani Kwale-kwale ya Kama da Wuta Yana tsaka da Tafiya a Ruwa a Jihar Neja

Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da wakilan ƙungiyar Musulmi ta kudu maso yammacin ƙasar suka kai masa ziyara ranar Juma’a a fadarsa da ke Villa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Talla

“Abu ne da ya shafi makomarmu. dole ne mu samar wa kanmu makoma mai kyau. Allah ba zai ɗora mana abin da ba za mu iya ba. Allah na da dalilinsa na kawo mu wannna matsayi, Abubuwa na ƙara tsananta, amma da yardarsa (Allah), za su yi sauƙi””.

Tinubu ya kuma kare matakinsa na cire tallafin man fetur da cewa ya yi hakan ne domin tseratar da ƙasar daga durƙushewa.

Shirin Dadin-Kowa ya sa samari son yin wuf da ni – Fati Harka

“Mun kwashe kimanin shekara 40 muna ta ƙoƙarin kauce wa matakin (cire tallafin mai). Za mu sha wahalar matakin a yanzu, to amma domin tseratar da ƙasarmu daga durƙushewa, ya zama wajibi mu cire tallafin mai”.

“A tarihin ƙasashen da suka ci gaba, babban abin da ya kawo musu ci gaban, shi ne ɗaukar matakai masu tsanani da shugabanninsu suka yi a lokacin da ya dace kan dalilan da suka dace”.

Talla

Shugaban ƙasar ya ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne, inda ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa daɗi na zuwa a gaba.

“Za mu yi bakin ƙoƙarinmu, kuma tattalin arzikinmu zai bunƙasa domin ci gaban ‘yan ƙasarmu, ina da tabbaci kan haka, za mu yi aiki don tabbatar da haka”, in Tinubu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...