Abdulmumini Kofa ya aika sakon ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Sarakunan Kano da Bichi

Date:

Daga Abubakar Y Abubakar

Babban Daraktan Hukumar Samar da gidaje ta Kasa Kuma Tsohon Dan Majalisar Kiru da Bebeji a zauren Majalisar Wakilai ta Kasa Hon. Abdulmumini Jibril Kofa ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga Gwamnan jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje da Sarakunan Kano da Bichi bisa Rasuwar Mahaifiyar Sarakunan Hajiya Maryam Ado Bayero ( Mai Babban Daki ).

Hon. Abdulmumini Jibril Kofa Wanda shi ne jagoran jam’iyyar APC na Kiru da Bebeji Kuma Jarman Bebeji ya bayyana rasuwar Mai Babban Daki a Matsayin babban Rashi ga al’ummar jihar Kano da Kasa baki Daya.

Jarman Bebejin yace labarin rasuwar Mai Babban Dakin ya girgiza shi sosai inda yayi Mata addu’ar samun Rahamar Allah madaukakin Sarki da Kuma fatan Allah ya gafarta Mata yasa aljanna ta zamo makoma a gareta.

“Ina Mika ta’aziyya ta ga Mai girma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da al’ummar jihar Kano Dana Kasa baki Daya”. Inji Kofa

Abdulmumini Jibril Kofa yace Hajiya Maryam Ado Bayero uwace ta Gari data sadaukar da Rayuwar ta wajen baiwa ya’yanta tarbiyya ta gari wacce yanzu al’umma yanzu duk suke amfana.

68 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...