Tarihin Alƙaliyar Kotun da Zata Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

An haifi mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay, shugaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano, a karshen shekarar 1950. Ta yi karatun firamare a Reagan Memorial Primary School, Iwaya, a jihar Legas.

 

Daga nan ta halarci Makarantar Grammar Girls ta St Louis, Owo a Jihar Ondo, Inda ta yi karatun sakandarenta a can.

Talla

A shekarar 1980 ta halarci Jami’ar Legas Akoka Legas inda ta yi digiri a fannin Shari’a Law sannan ta samu digiri. Ta Kuma halarci Makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya, dake Victoria Island, Legas tsakanin 1983 zuwa 1984. Ta kuma yi bautar kasa NYSC tsakanin 1984 zuwa 1984, Inda ta koyar a matsayin malamaa fannin a Kwalejin Fasaha ta Yaba, dake jihar Legas.

Cire tallafin mai: Yadda ta kasance a ganawar gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago

Ta Kuma taba zama Malama wata makarantar a Professional Accountancy Tutors (PAT) da Cibiyar Ma’aikatan Banki ta Najeriya (NIB).

Majiyar Kadaura24 ta Justice watch ta rawaito A shekarar 1986 ta halarci Jami’ar Legas inda ta samu digiri na biyu a fannin shari’a ta kasa da kasa da kuma diflomasiya (MILD) Kuma ta kammala a shekarar 1987.

Tsakanin 1987 zuwa 1993 ta yi aiki a ofishin Lauyoyi na Fola Akinrinsola da Co a Legas sannan ta kafa nata ofishin a shekarar 1993.

A shekara ta 2004, gwamnatin tarayyar Najeriya ta nada ta a matsayin mamba a kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazari da binchike harkokin Ruwa ta Najeriya (NIOMR), dake Victoria Island, a jihar Legas har zuwa shekara ta 2006, lokacin da aka Maida ita jihar Ondo.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano

An rantsar da ita a ranar 1 ga watan Agustan 2006 a matsayin alkalin babbar kotu a jihar Ondo, mukamin da take rike da shi har zuwa yau.

Ita mamba ce a kungiyar alƙalan shari’ar ‘yan gudun hijira ta duniya kuma mamba ce ta Ƙungiyar Alƙalai Mata ta Duniya. Ta zauna a matsayin mamba a kotun sauraron kararrakin zabe a jihohin Delta da Kogi a 2011 da 2015. A halin yanzu ita ce shugabar kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano.

Mai Shari’a Osadebay ta halarci tarukan karawa juna sani a gida Nigeria da kuma kasashen waje, Ita ce Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Yamma ta kungiyar sake fasalin Adalci ta Jihar Ondo (OSJRT) .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...