Ku daina baiwa ilimin boko muhimmanci fiye da na addini – Malam Yusuf Sha Iskawa ya gargadi dalibai

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kungiyar dalibai musulmi ta MSSN ta shawarci dalibai dasu zage damtse wajen neman ilimin addinin musulunci domin shi ne wanda zai amfani rayuwar su a duniya da lahira.

 

Shugaban Kungiyar reshen kwalejin kimiyya da fasaha ta Hussaini Adamu dake kazaure a jihar jigawa Malam Yusuf Musa Sha Iskawa ne ya bayyana hakan yayin taron bada lambar girmamawa ga tsofaffin shugabannin kungiyar wanda ya gudana a babban Dakin taro na kwalejin dake kazauren.

Talla

” Ilimin addini shi ne zai sa kasan waye ya halicceka da dalilin da yasa aka halicceka, da Kuma yadda zaka gudanar da ibada don ka sami sakamako mai Kyau tun daga nan duniya har zuwa gobe kiyama”. Inji Sha’Iskawa

Malam yusuf musa Abubakar gabatar da mukala yayin taron mai taken duk rayuwar da babu addini a cikinta asara ce kasancewar sai da ilimin addini ake iya bautawa Allah (SWT).

Da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Zamfara

“Kasancewar wannan makaranta makaranta ta hada mutane mabambantan addinai muyi kokari mubi koyarwar addini a yayin zamantakewar mu da mutane domin ribatar su izuwa addinin Allah”.

Kada mu rika tunani boko kadai muka zo yi, dole sai munyi kokari mun dage da karatun addini shi ilimin, domin shi na boko iyakarsa duniya shi kuma ilimin addini shi ne zai anfane mu tun a duniya harma a gobe kiyama”. A cewar shi

Daga karshe yaja hankalin sabbin shugabannin wannan kungiya masu sanya tsoran Allah a cikin zukatansu kuma suyi hakuri domin ita harkar shugabanci sai anyi hakuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...