Wata kungiya mai zaman kanta a Arewa, ta karrama hadimin Ganduje, Aminu Dahiru Ahmad

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Northern Women Youth and Students Congress, ta karrama mai daukar hoton shugaban jam’iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje, Hon. Aminu Dahiru Ahmad.

 

Kungiyar wadda ta haɗa dalibai matasa matan arewa tana aikin ta ne domin yaƙi da mummunar dabi’ar nan ta shaye-shayen miyagun kwayoyi Matasa a tsakanin mata a Arewacin Najeriya.

Sauya Sheka: Wike Ya Ziyarci Ganduje

Shugabannin Kungiyar sun mika lambar yabon ga Hon. Aminu Dahiru Ahmed a Abuja saboda irin kokarin da yake yi wajen tallafawa matasa maza da mata a Arewacin Najeriya.

Talla 

Kungiyar ta ce ta gamsu da yadda Hon. Aminu Dahiru Ahmed yake jajircewa wajen inganta rayuwar matasa ta hanyar basu shawarwari da tallafin yadda zasu gudanar da sana’o’in don su dogara da kawunansu.

 

Kungiyar ta ce Aminu Dahiru Ahmad matashi ne ya kamata duk matasa Nigeria su yi koyi da halin sa saboda yadda yake amfani da abun da Allah ya bashi wajen taimakawa matasa don su inganta rayuwar su.

Tallah

Aminu Dahiru Ahmad ya jima yana tallafawa matasa a fannonin da suka shafi karatunsu da Kuma sana’o’in, ko a kwanakin baya ma sai da kadaura24 ta rawaito ya biya kudin makaranta ga wasu matasa da suke Karatu a makarantun gaba da sakandire a Kano.

kungiyar ta samun sanya albarkar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin a matsayin su na iyaye ga Aminu Dahiru Ahmad.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...