Daga Zainab Kabir Kundila
Kungiyar kwallon kafa ta Kano pillers ta nada ya tsohon kwararren dan wasan kwallon kafan Nigeria Isa Abdullahi Jazino a matsayin jami’in tuntuba na kungiyar.
Takardar nadin Mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Mahmud Babangida, ta ce an nada Isa Abdullahi Jazinon ne Saboda ana ganin akwai gagarumar gudunmawa da zai iya baiwa kungiyar don ta kai ga nasara a wasannin ta.

” Muna fatan zaka yi amfani da kwarewar da kake da ita wajen bamu shawarwarin da zasu kara bunkasa kungiyar, musamman a wasannin za ta buga a nan gaba.
Shugaban NNPP na kasa, Farfesa Alkali ya yi murabus
Isa Abdullahi Jazino kwararren dan wasan kwallon kafa ne da ya buga wasanni a kungiyoyin kwallon kafa da dama a ciki da wajen Nigeria sama da shekaru 25 da suka gabata.
Sabon jami’in tuntubar ya kuma taba zama dan wasa a Kano Pillars da wasu kungiyoyi a Nigeria, sanann ya taba bugawa Nigeria wasa don haka ana ganin zai bada gudunmawa sosai wajen ciyar da kungiyar kwallon kafa ta Kano pillers gaba.