Alƙaliyar Kotun Sauraren Kararrakin Zabe a Kano ta Koka bisa yunkurin wani Babban Lauya na bata cin-hanci

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugabar kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar tarayya da ta dokoki a jihar Kano, Mai shari’a Flora Azinge, ta bayyana fushinta kan yunkurin wani babban Lauya mai muƙamin SAN, na neman ya ba ta cin hanci.

 

Da ta ke jawabi gabanin fara zaman sauraron ƙararraki a jiya Talata a Kano, alƙaliyar ta koka kan yadda manyan lauyoyi musamman ke aikata wannan mummunar dabi’a .

Talla

Ko da ya ke ba ta bayyana sunan babban lauyan ba, Ms Azinge ta ce SAN ɗin da ake magana a kai na da shari’a a gaban kotun.

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya ziyarci Kwankwaso har gida

“Babban Lauyan Najeriya da ke da shari’a a gabana ya na kokarin ba ni cin hanci. Tun jiya kudi ke yawo a wannan kotun. Duk wanda ya karɓi kuɗi a madadina, Allah zai hukunta shi da shi da zuri’arsa baki daya

“Suna ci gaba da zagin alkalai, suna zagin mu kullum a cikin jaridu, a kafafen yada labarai – cewa muna karbar rashawa.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta Soke Zaɓen Wani Dan Majalisar Tarayya a Kano

“Bari in sake jaddada muku cewa kada kowa ya sake tunkara ta da cin hanci. Na gamsu da abin da Allah ya ba ni, kuma ina da rufin asiri na,” in ji ta.

Sai dai Eyitayo Fatogun, SAN, wanda ya kasance a gaban kotun, ya tsaya a madadin dukkan lauyoyin da suka halarta, kuma ya bukaci alƙaliyar da ta kai ƙorafi ga hukumomin da suka dace.

Domin karfafa hujjar sa, babban lauyan ya ce ya ga inda shari’o’in da ake tuhumar alkalan da suka kasa gabatar da kararraki na irin wannan dabi’a ta cin hanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...