Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma wanda ya yiwa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben 2023 Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gidansa dake Abuja, ranar talata.
Rahotannin da kadaura24 ta samu sun ce tsofaffin yan takarar kujerar Shugaban kasa a 2023 sun yi ganawar sirri da juna, Ida ake hasashen abun da suka tattauna ba zai rasa nasaba da harkokin siyasa ba .

A baya dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Kwankwaso da Atiku wanda hakan ne yasa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar ta PDP gabanin zaɓen shekara ta 2023, inda ya koma jam’iyyar NNPP.
Wannan ziyara dai tasa wasu mutane sun fara tunanin ko akwai yiwuwar Kwankwason ya komawa jam’iyyar PDP sakamakon matsin lambar da ya fara fuskanta daga shugabannin jam’iyyar NNPP na kasa .
Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisun APC Na Kano Su Goyi Bayan Gwamna Abba Gida-gida
Wasu kuma suna ganin Kwankwaso zai iya komawa PDPn saboda kokarin komawa ko kawancen su da APC abun ya sami targaro, sakamakon kin bashi muƙamin minista kamar yadda akai ta hasashen hakan ko kuma saboda kasancewar Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar na kasa .
Amma wasu sun fara fargabar idan Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP a kano za’a iya samun rashin jituwa tsakanin Kwankwason da Malam Ibrahim Shekarau wanda a yanzu shike rike da jagorancin jam’iyyar PDP a kano.
A baya dai Shekarau da Kwankwaso sun taba haduwa a jam’iyyar APC Shekarau ya bar ta ya koma PDP, Inda bayan wasu yan Shekaru Kwankwason ya sake komawa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP , nan ma Shekarau ya fice daga PDPn bisa zargin uwar jam’iyyar ta kasa a wancan lokaci ta yi masa rashin adalci.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Kara Kudin Mai Fetur a Nigeria
Bayan Shekarau ya sake barin APC sun sake haduwa tsakanin Kwankwaso da Shekarau a jam’iyyar NNPP kafin daga bisa Shekarau ya fice ya sake komawa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP, hakan tasa ake fargabar kamar a wannan karon ma idan har Kwankwaso ya koma PDPn akwai yiwuwar Shekarau ya sake ficewa daga jam’iyyar sakamakon yadda kansu bata jikuwa waje guda da Kwankwaso.
Lokaci ne kadai zai iya bayyana hakikanin abun da zai kasance
Ga wasu daga cikin hotunan da hadin min Kwankwaso a kafafen yada labarai Saifullahi Hassan ya wallafa a sashihin shafin sa na Facebook.