Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Bola Tinubu yana duba yiwuwar dawo da “tallafin man fetur na wucin gadi” yayin da farashin danyen mai da kuma farashin musayar kudaden waje ke ci gaba da hauhawa .
Majiyar jaridar Kadaura24 ta The Cable ta rawaito har yanzu dai ba’a yanke hukunci na karshe akan batun ba, amma shawarar tana kan tebur ana tattaunawa, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin mawuyacin halin tattalin arziki bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

Tuni dai kungiyoyin kwadago suka yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ya gani idan har aka kara farashin man fetur din.
A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin Kenya ta sake dawo da tallafin man fetur domin dakile tashin farashin man fetur da kananzir da dizal a kasar.
Sauya Sheka: Wike Ya Ziyarci Ganduje
Matakin ya biyo bayan kazamar zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka shafe watanni ana yi kan tsadar rayuwa a kasar ya Kenya.
A ranar Litinin din da ta gabata ne kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya ce babu wani shiri na kara farashin man fetir din duk da tashin farashin danyen man da faduwar darajar Naira.
Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu
An fahimci hakan wani zaɓi ne ga Tinubu ya zabi ya kar ya kara kuɗin man ne a wannan gaba saboda halin da ake ciki, duk kuwa cewa dallalan man fetur din a Nigeria har yanzu basu ce komai ba akan lamarin.
Sai dai kuma rade-radin yunkurin karin farashin man ya haifar da firgici ga yan kasar, wanda hakan yasa mutane suka rika siyan man suna ajiyewa tun da sanyin safiyar ranar Talata.
A Najeriya, an kara farashin man fetur sau biyu tun bayan da aka soke tallafin. Daga nan ya tashi daga N185 zuwa sama da N500 a watan Mayu, sannan ya koma N617 a watan Yuli.
Har ila yau, farashin canjin Dala dai ya kai N950 a kasuwannin bayan fage wanda ba a taba ganin irinsa ba a Nigeria.
A ranar Litinin ne jaridar TheCable ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN na shirin aiwatar da wasu sabbin matakai na daidaita darajar Naira idan aka kwatanta da dala.
Makonni bayan da aka rantsar da Tinubu a matsayin zababben shugaban Najeriya, gwamnatinsa take cewa tana fito da wasu manufofi da dama a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar.
Amma duba da halin da tattalin arziƙin kasar ke ciki a yanzu, da alama waɗannan manufofin ba su haifar da sakamakon da ake tsammani ba.
Sai dai kadaura24 ta samu labarin cewa fadar shugaban kasa ta musanta wannan batun ta bakin Mai Magana da yawun Shugaban kasar Tope ajayi.