Sauya Sheka: Wike Ya Ziyarci Ganduje

Date:

Sauya Sheka: Wike Ya Ziyarci Ganduje

 

Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma wanda za’a nada a matsayin minista, Nyesom Wike, ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Gnaduje, a Abuja, ranar Talata.

 

Wike, wanda ya yaƙi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2023, ya sha musanta yunkurin shiga jam’iyya mai mulki ta APC.

Talla

A yayin wani taron godiya da aka shirya domin karrama shi jim kadan bayan mika mulki a Rivers, Gwamna Simi Fubara ya roki Wike da kada ya watsar da shi kod bayan ya shiga jam’iyya mai mulki.

Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisun APC Na Kano Su Goyi Bayan Gwamna Abba Gida-gida

“Muna ganin alamar cewa kamar kana so ka tafi ka barmu a wannan jam’iyyar, to idan ka tafi don Allah kada ka yi min nisa, kasancewar ku irin ku a kusa da ni zai taimakamin wajen yin abun da zai sa jihar mu ta cigaba”.in ji Fubara.

Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Kara Kudin Mai Fetur a Nigeria

Hasashen Wike zai fice daga jam’iyyar adawa ya kara karfi ne bayan da shugaba Bola Tinubu ya mika sunan sa ga majalisar domin nada shi a matsayin minista a gwamnatin sa.

Shugabannin jam’iyyar PDP sun nuna rashin jin dadinsu kan hakan tare da yin tunanin matakin hukunta tsohon gwamnan na Rivers.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...