Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce ta kaɗu da jin yunƙurin sojoji masu juyin mulki a Nijar na tuhumar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bazoum Mohamed da zargin babbar cin amanar ƙasa.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar sa’o’i bayan kalaman sojojin na yi wa Bazoum shari’a, Ecowas ta ce matakin wani takalar faɗa ne daga shugabannin sojin.

Ta kuma ce hakan ya ci karo da rahotannin da ake yaɗawa cewa sabbin masu mulkin Nijar ɗin sun nuna sha’awar bin hanyar masalaha don kawo ƙarshen dambarwar da ake ciki.
Ƴan majalisa a Ghana sun gargaɗi shugaban ƙasar kan tura sojoji Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.
Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar, zagon ƙasa.
Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta ƙasar.
Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu
Ana sa rai, ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za ta gudanar da wani taro ranar Litinin ɗin nan don ci gaba da matsa lamba ga sojojin juyin mulki su hau teburin tattaunawa, haka ita ma Majalisar Tsaro da Tabbatar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka za ta yi taron don tattaunawa a kan rikicin.
Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hamɓarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.