Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum a gaban kuliya saboda “cin amanar kasa” tare da yin silar shugabannin kasashen Afirka ta Yamma suka kakabawa kasar takunkumi.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta kakabawa Nijar takunkumai, sakamakon juyin mulkin da aka yi, kuma ba ta yanke hukuncin yin amfani da karfi ba, kan sojojin da suka hambarar da gwamnatin Dimokaradiyya ta Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli ba.

Kungiyar ECOWAS dai ta amince da aikewa da dakarun sojojin don a shirin ta na ko ta kwana don mayar da amfani da kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar cikin gaggawa amma duk da haka Kungiyar tana ta ci gaba da kokarin ganin an warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.
Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu
Shugabannin mulkin sojin Nijar sun ce za su tuhumi Bazoum da laifin cin amanar kasa da kuma kawo cikas ga tsaron ciki da wajen Nijar, a cewar wata sanarwa da Kanar-Major Amadou Abdramane ya karanta a gidan talabijin na kasar.
Sojoji Ba Su Taba Samun Buƙatar yin Juyin Mulki a Nigeria ba – Hedikwatar tsaro
Bazoum, mai shekaru 63, da iyalansa suna tsare a gidan shugaban kasar na Yamai tun bayan juyin mulkin, tare da nuna damuwar kasashen duniya kan yanayin da yake ciki.
” Tiani ya ce Kofar su a bude take don samun masalaha ta hanyar diflomasiyya da zaman lafiya wajen warware matsalar”, in ji Sheikh Bala Lau, kwana guda bayan tawagar malaman addinin musulunci na Najeriya sukai da shi a babban birnin Yamai.