Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kungiyar mafi girma ta yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta caccaki nadin ministocin da shugaba Bola Tinibu ya yi, inda ta ce rashin adalci ne ace mutane biyar kacal Tinubu zai baiwa mukaman ministoci a yankin kudu maso gabashin Nigeria.
Ohanaeze wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugabanta, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ta ce nadin ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma ka’idar zamantakewa a matsayin tarayya.

Kungiyar koli ta Igbo wadda ta ce ta damu da nade-naden ministocin da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan, ta tunatar da jiga-jigan siyasar Najeriya cewa dunkulewar Najeriya ba za ta samu ba sai an yiwa kowanne yanki adalci.
“A nadin, Kudu maso Gabas na da ministoci biyar ne kawai yayin da wasu shiyyoyi ke da ministoci tara har ma da masu 10,” a cewar Ohanaeze
Yanzu-Yanzu: Kotu ta Soke Zaɓen Wani Dan Majalisar Tarayya a Kano
“Ohanaeze Ndigbo na jin cewa rashin adalci ne kuma a cewa mutane biyar kacal aka ɗauka daga shiyyaarsu, haka Kungiyar Ohanaeze Ndigbo tace ta yi imani da kasancewar Nigeria a matsayin kasa daya dunkuliya, kuma hakan ba zata cigaba da tabbata ba har sai na yiwa kowacce shiyya adalci .
Shugaban Ohanaeze Janar ya tunatar da cewa gwamnatocin sojoji ne suka kirkiro jihohin da shiyyoyin siyasa 6 a Nigeria.
Juyin Mulkin Nijar: Muhammad Bazoum ya bayyana halin da ya shiga a hannun sojojin Nijar
“Yankin Kudu maso Gabas ya rage da jihohi biyar yayin da sauran shiyyoyin ke da mafi karancin jahohi shida, wannan lamarin ya sanya Kudu maso Gabas cikin tsaka mai wuya, ta fuskar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.
Ko da yake kungiyar ta Igbo ta bayyana cewa ba gwamnatin da ke ci a yanzu ce ta fara yi musu irin wannan rashin adalcin ba, amma ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya gyara lamarin tare da maido da adalci da daidaito a Najeriya.