Daga Hafsat Lawan Sheka
Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje, ya nada tsohon kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Muhammed Garba, a matsayin shugaban ma’aikatansa.
An bayyana nadin ne a cikin wata sanarwa da mai daukar hoton shugaban jam’iyyar APC na kasa Aminu Dahiru ya fitar.

Baya ga yin aiki a gwamnatin Ganduje a Kano na tsawon shekaru takwas, Muhammad Garba ya kuma rike mukamin sakataren yada labarai na ofishin mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Da dumi-dumi: Tinubu ya ba da umarnin sake ƙaƙaba wa Nijar takunkumai
Garba ya kuma kasance tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ). Ya kuma taba zama sakataren yada labarai na ofishin mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Tsohon kwamishinan yada labaran dai sun jima tare da tsohon gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kuma shi ne mukami na farko da sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya fara yi tun bayan rantsar da shi a mukamin a ƙarshen makon da ya gabata.