Daga Rahama Umar Kwaru
Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance Dr Mariya Mairiga Mahmoud a matsayin minista daga jihar Kano.
Dr Mariya dai ita ce ta maye gurbin Maryam Shetty da shugaba Tinubu ya cire sunanta a satin daya gabata.

Dr. Mariya Mahmoud Bunkure dai ta taba zama Kwamishiniya ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar kano lokacin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden shugabannin ma’aikatu 15
Sauyan sunan Maryam Shetty da Dr Mariya Mairiga ya janyo ce-ce-ku-ce shafukan sada zumunta.