Daga Rukayya Abdullahi Maida
Zauren Coronation mai dimbin tarihi da ke fadar gwamnatin jihar Kano, yana da mahimmaci na musamman a cikin abubuwan tarihi na birnin domin tun da farko an gina shi ne domin nadin sarautar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi.
Zauren wanda a cikin sa aka mika shaidar kama aiki ga Muhammad Sanusi II bayan ya gaji marigayi Alhaji Ado Bayero a shekarar 2014 a lokacin gwamnatin Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, yanzu haka ana ci gaba da gyare-gyare domin dawo da martabar dakin taron dake fadar gwamnatin jihar kano.

Wani muhimmin abu na wannan aikin na gyare-gyare shi ne mayar da hoton Sarki na 14, Malam Muhammadu Sanusi, a cikin zauren. Kamar yadda aka saba, hoton zai kasance a can har abada, don tunawa da dalilin samar da dakin taron.
Da dumi-dumi: Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar Nigeria
Gyaran da ake ci gaba da yi na nufin yi zauren Coronation gyaran fuska da ake bukata, tare da kiyaye muhimmancin tarihi da al’adunsa.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, ya tabbatar da cewa gyaran zauren ya hadar da dawo da hoton Sarkin na 14.
Zauren taro na Coronation yana da kima sosai ga al’ummar Kano, kuma gyaran da aka yi masa na nuna aniyar gwamnatin na kiyaye dimbin tarihi da al’adun gargajiya na mutanen Kano.
A safiyar wannan rana ce dai aka wayi gari da hotunan na tsohon Sarkin kano Muhammad Sanusi II, wanda ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.