Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A ranar Litinin ne gwamnatin tarayyar Nigeria, za ta gana da wakilan kungiyoyin kwadago a kokarinta na dakile yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasar ta kira a fadin kasar.
Sai dai kungiyar NLC ta shawarci ‘yan Nigeria da su tanadi kayan abinci da magunguna da sauran muhimman abubuwan bukata na yau da kullum a gidajensu, gabanin fara yajin aikin na kwanaki bakwai domin nuna adawa da cire tallafin man fetur da kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita a Nigeria.

“Gargadin ya zama dole saboda yajin aikin zai tsayar da komai a kasar, saboda za a takaita zirga-zirga sosai yayin da wuraren kasuwanci duk zasu zamo a kulle, kuma makarantu da wuraren kiwon lafiya za su kasance dukkaninsu a su.
Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta Kama Mutane 8, kan zargin batan biliyan 4 a KASCO
Mataimakin babban sakataren kungiyar ta NLC, Chris Onyeka, ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai , inda yace suma ‘yan kasar su rage yawan zirga-zirgar su domin gudun kada su fuskanci matsala.
Jaridar Sunday PUNCH ta rawaito cewa NLC ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki bakwai tare da barazanar fara yajin aikin gama gari a fadin Nigeria a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023. Kungiyar kwadago a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta zargi Tinubu. -Gwamnatin tarayya da gaza biyan bukatun da ta gabatar mata biyo bayan cire tallafin mai, wanda ya haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a Nigeria.
Shari’ar zaɓen gwamnan kano: Abba Gida-gida ya daukaka kara akan Shaidar APC na 32
Biyo bayan sanarwar yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC ta yi, nan take tawagar gwamnati ta kira taron gaggawa da kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar kwadago ta NLC a ranar Juma’a a fadar gwamnati.
Sai dai jami’an kungiyar da suka hada da kungiyar sun fice daga taron a fusace sakamakon gazawar da tawagar gwamnati ta yi.
Onyeka ya bayyana cewa kungiyar kwadagon za ta gana da gwamnati ranar litinin, inda ya kara da cewa sakamakon taron zai tabbatar da mataki na gaba.
Ya ce, “Ya kamata ‘yan Najeriya su shirya. Abin da muke cewa ke nan. Kasancewa cikin shiri yana nufin dole ne ku tanadi abinci a cikin gidan ku don gudun fadawa cikin kalubale