Matsalar tsaro tasa an Sanya dokar hana fita a Adamawa

Date:

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar ta-ɓaci ta tsawon sa’a 24 a fadin jihar.

Cikin wani saƙon da gwamnan ya wallafa a shafinsa ta twitter, ya ce an sanya dokar ne sakamakon ƙaruwar hare-haren da ɓata-gari ke kai wa mutane da kasuwanni a faɗin jihar.

Talla

Rahotonni daga jihar sun ce wasu ɓata-gari ne suka riƙa far wa mutane da makamai a birnin Yola tare da sace musu dukiyoyi a shagunansu.

Yajin aiki: Ku tanadi kayan abinci da magunguna a gidajenbku, NLC ga ‘yan Najeriya

Gwamna Fintiri ya ce an hana zirga-zirga a jihar, sai iya mutanen da ke ayyuka na musamman, waɗanda ke ɗauke da katin shaidar aiki.

Gwamnan wanda ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi biyayya ga dokar, ya ce tsaron lafiyar mutanen jihar shi ne babban abin da ya sanya a gaba.24

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...