Daga Zainab Kabir Kundila
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa tsohon kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya mika jerin sunayen ministoci ga majalisar dattawan Nigeria a ranar Alhamis.
Sergeant-At-Arms ne ya jagoranci Gbajabiamila zuwa cikin majalisar da misalin karfe 1:19 na rana bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa kuma sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, Michael Bamidele Opeyemi ya gabatar da batun a gaban majalisar.

Da yake mayar da martani bayan gabatar da wasikar, shugaban majalisar dattawa, Godswill Obot Akpabío ya karanta jerin sunayen wadanda Tinubu zai nada a matsayin ministocin sa.
Da dumi-dumi: Muhammad Bozoum ya Magantu Bayan yi Masa Juyin Mulki
Ga sunayen kamar haka :
1. Abubakar Momoh
2. Amb, Yusuf Tukar
3. Ahmad Dangiwa
4. Hannatu Musawa
5. Uche Nnaji
6. Beta Edu
7. Doris Uzoka
8. Dave Umahi
9. Nyesome Wike
10. Muhammadu Badaru
11. Nasir El-Rufai
12. Ekprikpe Ekpo
13. Nkiru Onyechiocha
14. Bumi Tunji Ojo
15. Stella Okotete
16. Uju Kennedy
17. Belo Muhammadu Gunyo
18. Dele Alake
19. Lateef Fagbemi
20. Muhammad Idri
21. Olawale Edu
22. Waheed Adebayoe Adelabu
23. Emman Suleman Ibrahim
24. Prof Ali Pate
25. Prof Joseph Utse
26. Abubakar Kyari
27. John Enoh
28. Sani Abubakar Danladi