Daga Khadija Aliyu
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Adolescent health Information Project (AHIP), tare da tallafin kungiyar Christian Aid, ta fara wani aiki, kan bukansa cigaba al’umma da raya kasa .
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun darakta mai kula da ayyukan AHIP Hajiya Mairo Bello, kuma ta aikowa kadaura24 a Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa, aikin mai taken “aikin da ya hada da samar da ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano” zai shafi makarantun mata a kananan hukumomin biyu da za’a fara gwajin shirin a kananan hukumomin Nasarawa da Kano Municipal.
Yadda Kansiloli suka dakatar da shugaban karamar hukuma a Kano
Daraktan, ta kara da cewa, matakin hada kan ‘ya’ya mata masu tasowa a jihar Kano, wata hanya ce ta tabbatar da shigar da marasa galihu cikin tsarin .
Ta ci gaba da cewa, hukumar gudanarwar manyan makarantun sakandire ta jihar Kano (KSSMB), ta amince da fara aikin a makarantu bakwai, GGSS Festival road, GGSS, Hassana Sufi, GGSS Sharada, GGASS Gama, GGASS Gwagwarwa, GGSS Giginyu da GGSS Gandun Albasa.
Da dumi-dumi: Kungiyar ƙwadago a Nigeria za ta fara yajin aiki a fadin kasar nan mako mai zuwa
Daraktan ya yi nuni da cewa, sun tuntubi malaman addini, al’umma, sarakunan gargajiya, da duk masu ruwa da tsaki a Kano, kafin fara shirin..
AHIP, kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa a shekarar 1989, kuma ta fara cikakken shirye-shiryen ci gaba ga matasa da mata a shekarar 1992, inda ta mai da hankali kan harkokin lafiya, zamantakewa da tattalin arziki da suka shafi matasa da mata musamman a Arewacin Najeriya.