Dangote ya gina rijiyoyin burtsatse guda 17 ga al’ummar jihar Kogi

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Kamfanin Dangote ya gina wkalla rijiyoyin burtsatse guda goma sha bakwai a cikin al’ummar da aka samar kamfanin siminti na Dangote da ke Obajana a jihar Kogi.

 

An samar da rijiyoyin burtsatsen ne a wuraren kamar Obajana shida (6), Oyo shida (6), Iwaa biyu (2) da Apata uku (3).

 

Da yake jawabi a taron bitar kwanaki biyu da kamfanin siminti na Dangote ya shiryawa ‘yan jaridu a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya, Babban Manajan kamfanin dake kula da al’amuran Al’umma da aiyukan na Musamman, Mista Ademola Adeyemi, ya ce an gudanar da ayyukan ruwan ne domin magance matsalolin ruwan sha ga al’umma musamman a lokacin da jama’a ke Kara yawa a inda aka samar da kamfanin.

Talla

Mista Adeyemi ya shaida wa manema labarai cewa, kamfanin yana da kyakkyawar alaka da al’ummomin da aka samar da shi a cikinsu, inda ya kara da cewa a baya-bayan nan ma kamfanin ya Samar da kayan aiki a asibitin da ke unguwar Iwaa don inganta rayuwar al’ummar yankin .

Yadda Kansiloli suka dakatar da shugaban karamar hukuma a Kano

A makon da ya gabata, Kamfanin ya aza harsashin gina ajujuwa guda 3 masu dauke da ofisoshi, dakin ma’aikaa da bandaki domin saukaka samar da makarantar sakandare a garin Oyo don inganta ilimi da rayuwar al’umma yankin da makwabtansu.

A yayin bikin aza harsashin ginin, an kuma kaddamar da sabuwar rijiyar burtsatse da aka kammala.

Majalisar dokokin Kano ta kaddamar da kwamitoci 38

A wajen taron, Baalo na Oyo, Oba Solomon Obahawu, ya yabawa kamfanin bisa bayar da gudunmawar ci gaban al’ummarsa.

Daraktan Kamfanin simintin na Dangote Mista JV Gungune, ya shaida wa manema labarai cewa, ana shirin samar da sana’o’in ne da nufin tallafa wa gwamnati a kokarinta na samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arzikin cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...