Daga Buhari Ali Abdullahi
Wata kungiya mai fafutukar tabbatar da adalci da yaki da cin hanci da rashawa tace al’umma suna da damar Kai korafi kan zargin cin hanci da rashawa akan wadanda suke wakiltarsu a zauren majalisu.
Guda cikin shugabannin kungiyar Muhammad Yusuf Musa ne ya bayyana hakan yayin da kungiyar su ta shirya wani taro ga al’ummar wasu kananan hukumomi a Kano.

“Akwai hanyoyi da yawa da ake bi wajen mika korafi kan Masu wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa wajen hukumomin da abun ya shafa don magance masu irin waccan mummunar dabi’a da wasu yan majalisu suke yi “. Inji Muhammad Yusuf Musa
Yunkurin rushe gidaje: Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano
Muhammad Yusuf ya ce al’ummar kananan hukumomin Gezawa, Munjibur da Gabasawa ne suka Sami horon a wannan karon .
Muhammad Yusuf Musa yace sun gudanar da taron ne domin wayarwa da mutane kai akan irin nauyin da yake kan wakilan da suka zaba har ma da yadda zasu shigar da korafin cin hanci da rashawa idan yafaru a yankunan su.
Musa ya ce domin karawa taron armashi sai da suka gayyaci jami’an hukumar EFCC da na I C P C don su yiwa al’ummar jawabi so sai kan hanyoyin da zasu bi domin shigar da korafin zargin cin hanci da rashawa.
Da suke bayyana jin dadinsu wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sunce tabbas sun Sami ilimi sosai sakamakon taron.