Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyar Kwallon Kafa ta Gidan gyaran Hali ta kasa Reshen Jihar Kano wato FC Kano Correctional Tigers ta fafata wasa tsakaninta da mazauna Gidan gyaran Hali na Kurmawa a jiya Juma’a.
A yayin wasan mazauna gidan gyaran halin dake kurmawa sun lallasa Kungiyar Ma’aikatan gidan gyaran halin reshen jihar Kano daci 7-6 .
Yadda Kamfanin UK ENTERTAINMENT Ya Shirya Sabon Fim Mai Dogon Zango Mai suna FATAKE
Wasan dai shi ne irinsa na Farko da aka gudanar dan taya murnar karin girma ga ma’aikatan gidan gyaran halin reshen Jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito ma’aikatan gidan gyaran hali reshen jihar Kano Sama Dubu daya ne suka samu karin girma a matakai daban-daban.
A karshe Kaftin din Kungiyar Kwallon Kafar ta Gidan gyaran hali reshen jihar Kano, Inspector Abbas Abubakar Musa ya yabawa yan wasan sa bisa namiji kokarin da su kayi a yayin wasan da su ka buga tsakaninsu da mazauna Gidan gyaran Halin dake Kurmawa.
Sanann ya yabawa suma mazauna gidan gyaran halin dake kurmawa bisa yadda suka buga wasan cikin farin ciki da annushuwa, kuma har suka taya ma’aikatan murnar karin girman.