Yadda Kamfanin UK ENTERTAINMENT Ya Shirya Sabon Fim Mai Dogon Zango Mai suna FATAKE

Date:

Daga Hafsat Abdullahi Muhd

 

Shugaban Kamfanin UK Entertainment Mal Umar Sani Lawal (Umar Uk) bayyana cewa sun shirya fim din FATAKE ne don al’ummar Hausawan duniya da iya kacin kano da Nigeria ba.

 

Umar Sani wanda aka sani da Umar UK ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai, kan sabon shirin kamfanin nasu mai dogon zango na FATAKE .

Tallah

U K ya bayyana cewar duba da takaita tunani waje guda da yawancin yan uwansa masu shirya Fim suke yi, ya sa suka yi dogon nazari wajen samar da wannan Fim mai dogon zango da za su karade kasashen Afirka ana shirya shi, wato Fatake.

“Duba da mahimmancin al’ ada da dabi’un kowanne rukunin da Hausa suke, shi ya saka duk kasar da suka muka je domin daukar wannan shiri muke amfani da jarumai na wannan ƙasar, domin samun abinda ake bukata irin na wannan yankin”. A cewar Umar UK

Wani rukuni na wadanda suka halarci taron kaddamar da fim din FATAKE

Umar ya kara da cewar sun kalli abubuwan da ke saka Hausawa barin kasashensu na asali, wanda ya hada da kasuwanci, neman ilmi, rigimar sarauta, da  dai sauransu.

 

Wadannan dalilai ne ya saka suka kulla zaren labarin nasu akan haka, wanda za a ga an fara da asalin in da Hausawa suke Nijeriya da Nijar daga nan mu kayi Ghana sai Nijar, Mali sai Kamaru, kuma dukkannin kasashen nan mun karaɗe ko ina a cikinsu duba da yan bambamcen karin harshe da ake samu.

Wani sashi na mahalarta taron kaddamar da fim din FATAKE

Da wadannan kadai za a ga an samu bambanci da yadda muke gabatar sauran shirye shiryen fina-finanmu a baya. In Ji Umar U k

Hakazalika mun kalli yadda Fataken da suke gudanar da al amuransu da kuma an kulla abinda matasan zamanin nan ke bukata, wato soyayya tare da Nishadantarwa.

 

Kai ko ba a gaya maka ba, daga jin sunan Fatake kasan akwai magana kunshe ciki.

A yayin walimar da kamfanin suka hada don kaddamar da sabon shirin, an samu halartar jagororin gwamnatin jihar Kano irin su shugaban ma aikantan fadar Gwamnatin jihar (Chief of Staff) Alhaji Shehu Sagagi da sauran jagororin gwamnati.

Sai manya manyan jaruman masana antar da masu shiryawa da masu bada umarni da sauran jama ar Kannywood

U K ya bayyana cewar duk wanda yake da bukatar kallon fim din Hausa da asalin Hausawan kasashen Afirika sai ya tara ranar 2/7/2023 a tashar Gaskia Tv Plus akan tauraron dan adam karfe 8 na dare agogon Ghana sai karfe 9:00 na dare agogon Nijeriya da Nijar.

Kuma ita wannan tasha ta GASKIA
TV da GASKIA PLUS s kyauta ce ake kallonsu a duk inda kake a adireshin
Satelite: badr7 @ 26°E
Frequency: 11010
Symbol rate: 27500
Polarisation: Vertical

Baya ga nan akwai tashar youtube dinmu mai suna UK Entertainment ko Gaskia Tv YouTube itama zamu dora muku wannan shirin Fatake akwai baya ga fina-finanmu da za a iya samu a ciki.

“Wato duk masu bibiyar shirye-shiryen kamfanin mu sun san dama irin ingantattun fina-finan da muka dade muna kawo muku, ga kuma wanda bai san fina-finanmu ba, kafin wannan ranar su garzaya su gane wa idon su”. Inji Umar UK

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...