Jerin gwanon motocin Tinubu ya haifar da cece-kuce a Nigeria

Date:

Bidiyon jerin gwano motocin da suka yi wa shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu rakiya a lokacin da ya sauka a jihar Legas ya tayar da kura, inda jama’a ke ta cece-kuce a shafukan sada zumunta.

 

Shaidu sun ce sabon shugaban kasar ya samu rakiyar motoci sama da dari bayan dawowa daga Birtaniya domin gudanar da bikin Babbar Sallah a Legas.

Tallah

Kazalika an ga gwamman motocin soji na masa rakiya a hanyoyin da aka rufe aka hana kowa wucewa, abin da ya haifar da gagarumin cunkoso.

Wannan ne dai karon farko da Bola Tinubu ya gabatar da Sallah idi a matsayin sa na sabon shugaban kasar Nigeria.

Tallah

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...