A baiwa kowa dama yayi takarar Gwamnan Kano shi ne adalci – Shekarau

Date:

Tsohon gwamnan Kano, kuma Sanata mai wakiltar Kano Ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwa a kan yadda wasu ‘yan siyasa a jihar ke ƙoƙarin farfaɗo da siyasar daba da aka jima da kawar da ita.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Sashen Hausa na BBC, inda ya ce babbar illa ce a ci gaba da yin hamayyar siyasa a Kano kamar yadda ake ganin wasu na yi, ta hanyar ɗaukar makamai suna far wa abokan hamayyarsu.

Yana magana ne kan batun fitar da wanda zai gaji gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje a zaɓen 2023, inda ya ce akwai bukatar shugabannin jam’iyyar APC na jihar su yi wa kowa adalci, kada a hana duk mai sha’awa tsayawa takara.

Ya ce “Babu laifi masu neman mukamai su fito, yau in masu neman gwamna sun kai mutum 100 karkashin jam’iyyar APC a Kano duk su fito, abun da kawai muke ganin zai zama illa shi ne ya zamana ana siyasar gaba, wannan ƙauyanci ne, shirme ne, kuma ya saɓa wa tarbiyyar addinin Musulunci ma”, in ji shi.

247 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...